‘Yan bindiga sun sace sarkin Kajuru a jihar Kaduna, Alhaji Alhassan Adamu da wasu mutane 13 a fadarsa da safiyar Lahadin nan. Rahotanni ...
‘Yan
bindiga sun sace sarkin Kajuru a jihar Kaduna, Alhaji Alhassan Adamu da wasu
mutane 13 a fadarsa da safiyar Lahadin nan.
Rahotanni
sun ce an yi awon gaba da sarkin ne da wani basarake, Alhaji Abubakar Kajuru
(Salaman Kajuru) da jikokinsa.
Wata
majiya ta ce ‘yan bindigar sun kai samame fadar sarkin ne da asubahin Lahadi,
kuma suka ci karensu ba babbaka, har suka dauke sarkin da mutane 13 daga
iyalansa.
Ana
fargbar abin da ka iya samun sarkin mai shekaru 85 duba da tsufa da ke da
nasaba da yawan shekarunsa, inda ake ganin ba zai iya jure takawa a kasa ba.
Wata
majiya ta daban ta tabbatar da cewa a ranar Juma’a Sarkin ya kira wani taron
gaggawa na tsaro, a kan labarin shirin sace shi.
Ya
zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukuma a game da batun sace sarkin na Kajuru.
-RFI Hausa
No comments