'Yan Bindiga Sun Yi Wa Ilimi Illa A Yankin Arewa, -Inji Janar Abdulsalam


 
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana damuwarsa da yin Allah wadai da yawaitar sace-sacen yara da ‘yan bindiga a fadin jihohin arewa ke yi, yana mai cewa hakan ya mai da karatun yankin baya zuwa shekaru 20.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar kamfen din dimokiradiyya da kare hakkin dan Adam, Kwamared Abdullahi Mohammed Jabi, a wata ziyarar girmamawa a gidansa da ke Uphill a Minna, babban birnin jihar Neja.

Janar Abdulsalami ya bayyana wadanda ke bayan satar yara daga makarantunsu a matsayin mugaye kuma marasa tsoron Allah, yana mai addu’ar Allah ya taba zukatansu don dakatar da munanan ayyukan.

Ya ce ayyukan ‘yan ta’addan ci baya ne ga ci gaban ilimi da ci gaban tattalin arzikin arewa.

Post a Comment

0 Comments