Wani rikici tsakanin jami'an rundunar sojin saman Nijeriya da ''yan
jagaliya' a Legas ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan kasuwa uku. Mutane da yawa sun
samu raunuka a rikicin da aka yi a kasuwar Ladipo da ke unguwar Mushin a jihar
ta Legas ranar Talata kamar yadda Bbc Hausa ta labarto.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya tursasa wa 'yan kasuwa rufe
sana'o'insu.
Kawo yanzu ba a san dalilin aukuwar rikicin ba,amma wasu da suka
shaida lamarin sun ce sojoji da 'yan sanda sun mamaye kasuwar kuma sun dakile
tashin hankalin.
0 Comments