Hukumomin Nijeriya sun ce akalla mutane 350 suka mutu sakamakon hadurran kwale kwale da aka samu a cikin kasar a shekarar 2020, abinda ke ...
Hukumomin
Nijeriya sun ce akalla mutane 350 suka mutu sakamakon hadurran kwale kwale da
aka samu a cikin kasar a shekarar 2020, abinda ke nuna yadda ake samun karuwar
hadura a sufurin jiragen ruwa a kasar.
Shugaban
majalisar gudanarwar Hukumar HYPPARDEC dake kula da yankunan dake samar da
wutar lantarki Joseph Ityav ya bayyana haka a Borgu dake Jihar Niger.
Ityav
wanda ya ziyarci Malale dake karamar Hukumar Borgu domin kaddamar da shirin
sare itatuwa da kuma dattin da suka mamaye kogin Kainji da Shiroro ya danganta
hadurran da rashin ingancin kwale kwalen da ake amfani da su da dibar mutanen
da suka wuce kima da kuma rashin amfani da rigar dake hana mutane nitsewa a
cikin ruwa sai kuma itatuwan dake tare hanyar da kwale kwalen ke bi.
Shugaban
majalisar yace sare itatuwa da kuma kwashe sharar dake tare hanyoyin da kwale
kwale ke bi zai taimaka wajen rage wahalar da mutanen dake zama a kusa da bakin
ruwa ke fuskanta.
Daraktan
Hukumar HYPPARDEC Abubakar Yelwa yace za suyi iya bakin kokarin su wajen shawo
kan matsalolin dake haifar da hadura a Kainji da Shiroro.
A
shekarar 1964 gwamnatin Najeriya ta gina madatsaruwan Kainji akan kogin Naija
akan kudi dala miliyan 209 kuma aka fara aiki da shi a shekarar 1968, yayin da
aka gina madatsar ruwan Shiroro a shekarar 1983.
A
ranar 27 ga watan Mayu kwale kwalen dake dauke da mutane 160 ya kife a Warrah
dake Jihar Niger inda aka tsamo gawarwaki 97, sauran mutanen kuma suka bata.
No comments