Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: 'Yan Bindiga Sun Saki Sarkin Kajuru Mai Shekara 85

  Bayanai daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa 'yan bindigar da suka sace Sarkin Kajuru Alhaji Alha...

 


Bayanai daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa 'yan bindigar da suka sace Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu sun sake shi.

Babban dan Sarkin, wanda kuma shi ne Madakin Kajuru Alhaji Musa Alhassan Adamu, ya tabbatar wa BBC Hausa cewa an saki mahaifin nasu dazun nan.

A cewarsa, suna zaune a gida da rana sai kawai suka ga sarkin ya shigo.

Sai dai ya kara da cewa ba a saki sauran mutum 13 da aka sace tare da sarkin ba.

Alhaji Musa Alhassan ya ce mahaifin nasu yana cikin koshin lafiya kuma ya shiga wanka inda suke jira ya fito sanna su kai shi asibiti domin a duba lafiyarsa.

Ya ce mazauna garin suna ta murna sakamakon sakin sarkinsu.

Da tsakar daren Lahadi ne wasu 'yan bindiga a kan babura suka kai hari kan masarautar Kajuru inda suka sace sarkin, mai shekara 85 tare da mutum 13, ciki har da jariri.

Bayanai sun nuna cewa sarkin ya gudanar da taro ranar Juma'a kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa.

No comments