Za A Bude Kantina A Saudiyya A Lokutan Da Ake Gudanar Da Salloli

 


Za a bude kantina da sana'o'i a Saudiyya a lokutan Sallah, a wani mataki da ya yi kama da sassauta dokokin cutar korona a masarautar.

Wata sanarwa da ta fito daga Ma'aikatar Kasuwanci ta Saudiyya ta ce matakin na cikin matakan da aka dauka saboda cutar korona, don takaita taron mutane da ke cincirindo a lokacin da shaguna suke a rufe a lokacin da a ke gudanar da salloli a masallaci.

Ba a sani ba ko wannan matakin zai zama na din-din-din amma wani mai sa ido kan al'amuran Saudiyya ya ce mataki ne mai muhimmanci.


Post a Comment

0 Comments