ZARGI: Majalisar Kano Ta Dage Zamanta Da Muhuyi Magaji

 


Majalisar Kano ta dage zaman da ta shirya yi na Muhuyi Magaji Rimin Gado ya bayyana gabanta sai baba ta gani.

Wannan na zuwa ne bayan rashin bayyanar Muhuyin a gaban kwamitin a yau.

A cewar lauyansa bai sami amsa gayyatar ba saboda rashin lafiya da yake fama da ita, wanda yake ganin likita a wani asibiti a Abuja.

Sannan ya ce kawo yanzu ba a bai wa muhuyi jeirin tuhume-tuhumen da ake yi masa ba.


Post a Comment

0 Comments