Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

A Shirye Nake Na Sake Garambawul A Bangaren Tsaro, Inji Shugaba Buhari

  Daga Muhammad A. Dalhatu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin iya bakin kokarin sa domin shawo kan matsalar tsaron da ta add...

 


Daga Muhammad A. Dalhatu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin iya bakin kokarin sa domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi kasar inda yake cewa ba zai yarda ya bar gwamnati a matsayin wanda ya gaza ba kamar yadda Rfi Hausa ta labarto.

Buhari ya ce a shirye yake ya gudanar da karin sauye sauye a bangaren tsaron kasar domin ganin an cimma biyan bukata wajen kare lafiya da dukiyoyin jama’a idan bukatar haka ta taso.

Mai baiwa shugaban shawara akan harkokin tsaro Janar Babagana Monguno ya bayyana wannan matsayin bayan taron majalisar tsaro da aka yi inda shugabannin suka tattauna halin da ake ciki da kuma irin nasarorin da ake samu sakamakon nada sabbin hafsoshin soji da ‘yan sandan da aka yi.

Monguno ya ce mika kan da daruruwan mayakan boko haram ke yi a hannun sojojin Nijeriya na daya daga cikin nasarorin da gwamnati ke samu wajen yaki da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin kasar, yayin da shugaban kasa ya yaba da yadda ake samun hadin kai sosai tsakanin hukumomin tsaron da ake da su sabanin yadda abin yake a shekarun baya.

Rikicin Boko haram da ‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu na daga cikin matsalolin tsaron da suka addabi Nijeriya, inda yanzu haka ake garkuwa da daruruwan mutane cikin su harda da daliban makarantu a jihohin Neja da Kaduna da Kebbi da kuma Katsina.

Ko a karshen makon jiya sai da aka samu rikicin dake da nasaba da addini a Jihar Filato lokacin da aka tare wasu matafiya a birnin Jos inda aka kashe sama da 30 abin da ya kai ga samun wasu kashe kashe a sassan birnin.


No comments