BBC Hausa; Ƙungiyar agaji ta kasa da kasa ICRC ta ce sama da mutu dubu 44 yanzu haka sun ɓata a sassan Afirka - sama da kashi 45 cikin 10...
BBC Hausa; Ƙungiyar agaji ta kasa da
kasa ICRC ta ce sama da mutu dubu 44 yanzu haka sun ɓata a sassan Afirka - sama
da kashi 45 cikin 100 na wannan adadi yara ne.
ICRC ta ce kashi 82 cikin 100 na
mutanen da ta dau rajistar ɓatawarsu sun fito ne daga ƙasahe bakwai da ke fama
da rikicin ƴan bindiga.
A wata sanawar da ta fitar kan ranar
tunawa da mutanen da suka bata a duniya a wannan Litinin din, ICRC ta ce sama
da rabin wannan adadi na mutane da suka ɓata ƴan Najeriya ne.
Sauran ƙasashen da aka samu ɓatarwa
mutanen sun hada da Ethiopia da Sudan ta Kudu da Somalia da Libya da DR Congo
da kuma Kamaru.
Hukumar ta ce nahiyar Afirka na
ganin karuwar mutanen da ke ɓatawa a shekarun baya-bayanan saboda rashin zaman
lafiya da wasu rigingimun.
Sannan yanayin da ake na annobar
korona na dakile kokarin binciko su domin sake sadasu da iyalansu.
No comments