Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Al'ummar Jibia Sun Sha Alwashin Maka Hukumar Kwastam A Kotu

Daga Abdulrazak Ahmad Jibia Biyo bayan sanadiyyar mutuwar mutane akalla 10 da raunata akalla 20 da  jami'an Kwastam suka yi a ranar 9 ga...


Daga Abdulrazak Ahmad Jibia

Biyo bayan sanadiyyar mutuwar mutane akalla 10 da raunata akalla 20 da  jami'an Kwastam suka yi a ranar 9 ga Agustan 2021 a garin Jibia na kara karamar hukumar ta Jibia ta jihar Katsina, an samu korafafe-korafe da dama daga bangarorin al'ummar garin da makwabta wadanda suka hada da: shugabanni na siyasa da Sarauta, 'yan kasuwa, da sauransu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa a ranar Juma'a 27 ga Agustan shekarar, gamayyar kungiyoyin fararen hula reshen karamar hukumar a karkashin jagorancin kungiyar "Masoya Ci Gaban Karamar Hukumar Jibia" suka gudanar da taron manema labarai inda suka bayyana matsalolin da karamar hukumar ke fuskanta.

Shugaban kungiyar, Malam Sulaiman Kalalu, da Ma'aji Alhaji Bishir Adamu, sun nuna damuwarsu game da mummunan halin da 'yan kasuwa suke ciki na karamar hukumar. 

Memba a kungiyar "JIBIA FIRST", Yusuf Abdullahi (Chana'a), ya musanta jawabin da hukumar Kwastam ta yi, inda ta karyata labaran dake yawo a kafafen sadarwar zamani cewa "Hukumar ta hana shigar da kayayyakin da aka samar a Nijeriya daga birnin Katsina zuwa Jibia". Ya kuma kara da cewa akan idonsa lamarin ya faru. 

Wani mazaunin garin Jibia, Isah Yahuza Dabo, ya nuna damuwarsa game da yadda jami'an tsaro suke amfani da kananan yara (Fararen Hula) wajen gudanar da ayyukansu, kuma ya bayyana makomarsu da cewa; "a lokacin da suka rasa aikin" a matsayin annoba a cikin al'umma.

Shugaban kungiyar NYCN reshen karamar hukumar Jibia, Jamilu Hamisu Shalla, ya bukaci gwamnatin Nijeriya da ta kawar da dokar takaita bude gidajen man fetur da ta saka a kananan hukumomin da suke a iyakokin kasar. Ya kara da cewa "Yin haka zai taimaka wajen magance matsalar tattalin arziki dake addabar kasar."

Da yake jawabi Ambasadan zaman lafiya na gidauniyar "GLOBAL PEACE FOUNDATION" Kwamared Gidado Sulaiman Farfaru, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta yi gaggawar magance matsalolin da karamar hukumar Jibia ke fuskanta. Kuma ya tabbatar cewa matukar hukumar Kwastam ba ta takaita cin zarafin da suke yi wa alummar Jibia ba, a shirye suke da su hada kai da manya-manyan kungiyoyin fararen hula na Nijeriya domin shigar da kararsu a kotu.


No comments