Nijeriya ba karbi kunshin alluran rigakafin annobar Korona na kamfanin Moderna guda miliyan 4 daga Amurka, a yayin da kasar ke kara azam...
Nijeriya ba karbi kunshin alluran rigakafin annobar Korona na kamfanin Moderna guda miliyan 4 daga Amurka, a yayin da kasar ke kara azama wajen kokarin dakile yaduwar cutar da ta sake kunno kai a karo na 3.
Jami’a daga ofishin asusun kula da kananan yara na duniya a Najeriya ne suka karbi wadannan alluran da suka isa kasar cikin jiragen sama 2, a filin tashi da saukan jiragen sama na Abuja.
Wannan ne karo na biyu da alluran rigakafin wannan shu’umin cuta ke isowa kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afrika.
A watan Maris, kasar ta karbi alluran rigakafi har guda miliyan 4, a karkashin shirin wadata matalautan kasashe da rigakafin Korona na COVAX.
No comments