Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Gurfanar Da Wata Matar Aure A Kotu Bisa Zargin Mayar Da Gidanta Zuwa Gidan Karuwai A Zariya

Daga Muhammad A. Dalhatu Mahaifiyar ‘ya’ya biyu, Altine Abdullahi a ranar Talata ta bayyana a gaban Kotun Majistare dake Kofar Fada cikin ga...


Daga Muhammad A. Dalhatu

Mahaifiyar ‘ya’ya biyu, Altine Abdullahi a ranar Talata ta bayyana a gaban Kotun Majistare dake Kofar Fada cikin garin Zariya ta jihar Kaduna bisa zarginta da yadda ta maida gidanta ya zama gidan karuwai. 

 Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya labarto cewa; ‘yan sanda na tuhumar Altine Abdullahi da Mohammed Yasir da hadin baki, aikata zina da kuma garkuwa da mutum wanda hakan ya sabawa sashe na 59, 230 da kuma 368 na dokar ‘Penal code’. 

Mai shigar da karar, Insfekta Abdullahi Sarki, ya shaidawa kotun cewa ‘yan sandan sun kammala bincikensu dangane da tuhumar da suke yi kuma a shirye suke su ci gaba da bibiyar lamarin. 

Sai dai Alkaliyar Kotun, Zainab Garba, ta mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sanda a Kaduna domin ci gaba da bincike.

"Ba zan iya fahimtar yadda mai ƙaramin shekaru zai iya fuskantar shari'ar aikata zina ba," in ji ta.

A cikin Rahoton Farko wato FIR, mai gabatar da karar ya yi zargin cewa a ranar 10 ga watan Agusta, da misalin awanni 1300, Bello Shehu dake lamba 97 Rimin Doko, a cikin Birnin Zariya, shi ne ya bada rahoton cewa Yasir ya tafi da 'yarsa mai shekaru 15 (an sakaya sunanta) zuwa gidan Altine Abdullahi dake Gwargwaje duk a Zariya.

Masu shigar da karar har wala yau na zargin Altine Abdullahi da bai wa Yasir daki akan Naira Dubu Daya (1, 000) inda ya yi zina da yarinyar mai kananan shekaru kuma har ya yi mata ciki. 


No comments