Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya kafa dokar hana fita ta sa’oi 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa domin shawo kan matsalolin tsar...
Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya kafa dokar hana fita ta sa’oi 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankin tun bayan kisan da aka yiwa wasu matafiya sama da 30 jiya a Unguwar Gada Biyu.
Sanarwar da Daraktan yada labaran Gwamna Dr Makut Simon Macham ya sanyawa hannu tace daga karfe 2 na yammacin yau 15 ga watan Agustan shekarar 2021 ba’a bukatar ganin jama’a a wajen gidajen su.
Macham yace bukatar haka ta biyo bayan irin zaman zulumin da aka shiga da kuma barazanar barkewar rikicin da zai kaiga rasa rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamna Lalong ya bukaci jama’ar jihar da su mutunta dokar domin ci gaba da zama a gidajen su dan baiwa jami’an tsaro damar gudanar da aikin su na tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Sanarwar gwamnatin tace dokar hana fitar ta sa’oi 24 da zata fara aiki daga karfe 2 na yammacin yau zata ci gaba da zama a karamar hukumar Jos ta Arewa har zuwa abinda hali zai yi.
Rahotanni sun ce matsalar da aka samu jiya na kashe matafiyan da suke wucewa a mota ta cikin birnin Jos ta haifar da zulumi da kuma rashin kwanciyar hankali a fadin birnin.
Majiyoyi a garin na Jos sun ce anji karar harbe harbe a wasu unguwanni, yayin da kwamishinan yada labarai Dan Manjang ya shaida mana cewar tuni aka baza jami’an tsaro bayan aukuwar lamarin domin tabbatar da zaman lafiya, yayin da aka kama wasu daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu wajen kai harin.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicin sa da kisan a sanarwar da mai Magana da yawun sa Garba Shehu ya rabawa manema labarai, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace abin kunya ne kisan da aka yiwa matafiyan.
No comments