Rahoton BBC Hausa Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya, ya ce harin da aka kai a Kwalejin koyar da aikin soja ...
Malam
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya, ya ce harin da aka kai a
Kwalejin koyar da aikin soja ta NDA a Kaduna na iya zama siyasa da kuma nufin
kunyata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A
ranar Talata ne wasu Æ´an bindiga suka kai hari Kwalejin Sojoji da ke birnin
Kaduna, kuma bayanai sun ce 'yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka
sace soja guda É—aya yayin harin da suka kai da tsakar dare.
Harin
ya ja hankali a Najeriya tare da haifar da damuwa kan karuwar matsalar tsaro a
ƙasar.
Da
yake mayar da martani kan harin a wata hira da gidan talabijin ta Channels ya
yi da shi ranar Laraba, Malam Garba Shehu ya ce abubuwa da dama kan iya zama
dalilin kai harin.
Kuma
Garba Shehu wanda ya ce shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da harin ya ce
"wasu na iya kitsa harin domin kunyata gwamnatin Buhari saboda nasarorin
da aka samu a yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da kuma ƴan fashin daji.
Ya
kuma ce bita da ƙullin siyasa na iya zama dalilin kai harin.
"A
yanayi na siyasa, mutane na iya amfani da wannan damar daga wannan mummunan
al'amari, ba za a iya cire wannan tsammanin ba" in ji shi.
Ya
ce fadar shugaban kasar na sa ran sojoji za su yi bincike sosai domin gano abin
da ya faru da dalilin faruwarsu tare da bayyana sakamakon bincikensu.
Masu
sharhi kan lamuran tsaro dai na ganin harin a matsayin wani abin kunya ga
sojoji wadanda a baya, duk karfin halin dan bindiga, ba zai daddara ya kai musu
hari ba.
Wasu
rahotannin kafafen yada labarai na Najeriya, da ba a tabbatar ba na cewar an
tsinci gawar sojan da 'yan fashi daji suka sace a kwalejin NDA.
Amma
rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata wasu rahotannin da suka ce sojojin da ke
bakin aikin tsaron Kwalejin Horon Sojoji ta NDA bacci suke lokacin da Æ´an
bindiga suka kai hari wanda ya kai ga kashe sojoji biyu da sace soja É—aya.
Sanarwar
da babban jami'in yaÉ—a labarai na rundunar sojin ya fitar Manjo Janar Benjamin
Olufemi Sawyerr ya ce labarin da jaridar Cable ta wallafa ba gaskiya ba ne inda
ya ƙalubalanci jaridar ta bayar da shaidar da ke tabbatar da jami'an sojin suna
bacci lokacin da Æ´an bindigar suka kawo hari.
Labarin
da ake yaÉ—awa na cewa bacci ne ya kwashi jami'an da ke kula da kamarori na
tsaro lokacin da Æ´an bindigar suka abka kwalejin NDA.
Rundunar
sojin ta ce babban hafsan sojin Najeriya da hukumomin NDA sun kaddamar da
bincike domin gano yadda har aka samu matsalar da ta ba Æ´an bindiga damar shiga
kwalejin.
No comments