An Kashe Matafiya 22 A Jos, Gwamnati Ta Yi Allah-Wadai


Rahotanni daga Jihar Filato ta ce yanzu haka ana zaman dar-dar a birnin Jos sakamakon wani hari da aka kai wa wadansu matafiyan da suka fito daga Bauchi akan hanyar su ta zuwa kudancin kasar inda aka kashe mutane 22.

Bayanai sun ce an tare motocin matafiyan ne guda 6 wadanda ke dauke da fasinjojin da akasarin su Fulani ne a Unguwar Gada Biyu bayan sun fito taron zikiri a Bauchi inda aka kai musu harin da aka kashe wasu da dama, yayin da wasu kuma suka samu raunuka.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Ubah Ogaba ya ce akalla mutane 22 aka kashe a harin.

Wata majiya ta ce matafiyan sun gamu da fushin mutanen ne dake korafi dangane da hare-haren da ake kai wa jama’ar su a Yankin karamar hukumar Bassa wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Majiyar mu ta shaida mana cewar tuni aka tura jami’an tsaron soja da ‘yan Sanda domin tabbatar da zaman lafiya a unguwar, yayin da ake ci gaba da zaman zulumi a birnin Jos da kewayensa kamar yadda RFI Hausa suka labarto.

Daya daga cikin matafiyan da ya tsallake rijiya da baya Muhammad Ibrahim ya ce sun fito taron zikirin sabuwar shekarar Islama ce da aka yi a Masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake garin Bauchi.

Kwamishinan yada labaran Jihar Filato, Dan Manjang ya tabbatar da aukuwar lamari da kuma nuna fushin gwamnatin jihar akan abin da ya faru, inda ya ce tuni aka kama wasu mutanen da ake zargin suna da hannu wajen kai harin.

Manjang ya kuma shaida mana cewar jami’an tsaro suna can suna gudanar da aikin su a Unguwar Gada Biyu da aka samu matsalar, kuma an kai wadanda suka samu raunuka asibitin gwamnati inda ake kula da su.

Wakilin RFI Hausa a Jos Muhammad Tasiu Zakari ya ce rundunar sojin dake aikin samar da zaman lafiya ta ce za ta gabatar da sanarwa nan gaba akan abin da ya faru.

Ko a makon jiya sai da aka samu irin wannan tashin hankali wanda ya kai ga kona motocin matafiya da kuma kashe wasu a kusa da shataletalen filin Polo dake Unguwar Gada Biyu.

Yunkurin tabbatar da zaman lafiyar da gwamnatin jihar Filato ke kokari na ci gaba da samun zagon kasa daga mutanen dake kai hare-hare akan jama’a a kauyuka da biranen jihar.

A makon jiya Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya jagoranci taron Majalisar tsaro wanda ya kunshi shugabannin rundunonin tsaron jihar da Sarakuna inda suka bukaci kara kaimi wajen magance hare haren da ake samu a Jihar.Post a Comment

0 Comments