An Yi Artabu Tsakanin Sojoji Da ‘Yan Bindiga A Filato

 


Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yan bindiga  shida bayan ‘yan bindigar sun kashe wadansu 'yan sanda uku masu farin kaya, wadanda suka je bincike a yankin karamar hukumar Mangu.

‘Yan ta’adda shida ne rundunar sojin da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta ta STF ta halaka yayin da jami’an ‘yan sanda uku suka rasa ransu.

Lamarin ya faru ne a wani artabu da bata garin a yankin Bwai dake karamar hukumar Mangu a jihar.

Kakakin rundunar tsaro ta Special Task Force (STF) a jihar, Manjo Ishaku Takwa ya ce, rundunar ta sami kiran neman agaji ne daga jami’an ‘yan sandan na musamman dake binciken masu laifi, a lokacin da suka je bincike ‘yan bindigar suka auka musu suka kashe ‘jami’an ‘yan sanda uku suka arce da makamansu.


Post a Comment

0 Comments