Ministan Sufurin Nijeriya, Rotimi Amaechi ya ce jami’an gwamnati mai ci na sata a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a boye s...
Ministan
Sufurin Nijeriya, Rotimi Amaechi ya ce jami’an gwamnati mai ci na sata a
karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a boye sabanin yadda aka ake yi
a fili lokacin gwamnatocin da suka gabata.
Amaechi
ya ce sabanin yadda aka saba tafiyar da gwamnatocin da suka shude a Nijeriya,
wannan gwamnatin da take ci ta APC ta yi iya bakin kokarin ta wajen dakile almubazaranci
da dukiyar jama’a da kuma hukunta wadanda suka yi rub da ciki da kudaden
talakawa.
Kamar
yadda Rfi Hausa suka lanarto, tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya ce a shekarun da
suka gabata, za ka ga mutane sun zama Attajirai dare daya ba tare da an san su
da wata sana’a ba, kuma babu wanda ya hukunta su, amma a karkashin mulkin
Buhari ba a samun haka.
Amaechi
ya ce cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a karkashin gwamnatocin Nijeriya
da suka shude, ta yadda za ka ga mutane suna bushasha da dukiyar da ba a san
inda suka samo ta ba a bainar jama’a, amma a karkashin wannan gwamnati idan za
ka yi sata sai dai ka yi ta a boye, kuma idan an kama ka, zaka fuskanci fushin
hukuma.
Wannan
matsayi na ministan a hirar da ya yi da jaridar Daily Trust na zuwa ne a daidai
lokacin da wasu ‘yan Nijeriya ke zargin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
bar wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa na facaka da dukiyar jama’a.
Daga
cikin wadanda ake zargi da irin wannan badakalar harda wasu ministoci da
gwamnoni da shugabannin manyan hukumomin gwamnati.
No comments