Ashura: ‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Shi’a 2 A Sakkwato A Yayin Harin Da Suka Kai Musu

 

Daya daga cikin wadanda 'yan sanda suka raunata.

 ‘Yan sandan Nijeriya sun afka ma mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya, da aka fi sani da ‘yan Shi’a a yau Alhamis a garin Sakkwato a yayin da suka fito muzaharar ranar Ashura kamar yadda suka saba a  duk shekara.

Lamarin ya auku ne a daidai titin Mabera Kantin Sani/ Mabera Dange dake yankin Mabera a jihar a Sakkwato kamar yadda ganau ya tabbatarwa da MADOGARA.

Mabiya Shi’ar sun fito dandazonsu cikin lumana suna tafe suna rera wakokin juyayin tunawa da kashe jikan Manzon Allah (S), Sayyidina Husaini kamar yadda suka saba a kowacce ranar 10 ga watan Muharram. 

A bidiyon da MADOGARA ta kalla kana jiyo karar harsashi mai rai da kuma tiyagas wadanda jami’an tsaron suka yi amfani da shi akan mabiya Shi’ar. 

Wata majiya ta shaida mana cewa; ‘yan sandan sun kashe mutum biyu, inda aka bayyana daya daga cikin wadanda aka kashe da Hassan Abubakar. 

Sannan majiyarmu ta labarta mana cewa an raunata mutane da dama da ya zuwa yanzu ba a tantance yawansu ba.

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani daga dukkanin bangarorin biyu. 

Jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin Arewa maso yamma da ke fama da matsalar ‘yan bindiga, masu garkuwa da jama’a da kuma masu fyade. 


Post a Comment

0 Comments