A jiya Talata ne aka rantsar da sabon shugaban kasar Iran, Ibrahim Raïssi, kan karagar shugabancin kasar Iran. Raïssi ya bayyana cewa, g...
A jiya Talata ne aka rantsar da sabon
shugaban kasar Iran, Ibrahim Raïssi, kan karagar shugabancin kasar Iran.
Raïssi ya bayyana cewa, gwamnatinsa
za ta yi iya yinta, wajen ganin ta kawo karshen
takunkuman kariyar tattalin arizikin da kasar Amruka ta kakaba mata, ba
tare da ta nemi taimakon kasashen
ketare, wajen sake farfado da tattalin arizikin kasar da suka fuskanci koma
baya ba.
Tsohon shugaban hukumar shari’ar kasar, Ibrahim Raïssi, mai shekaru
60 a duniya, a jiya ne a hukumance ya
karbi rantsuwar fara aikin wa’adin mulkin shekaru 4, bayan
tabbatar da zabensa, da babban jagoran kare juyin juya halin mulkin musuluncin
kasar Ayatollah Ali Khamenei ya yi.
A lokacin da yake jawabi bayan
rantsar da shi, Raissi ya ce zai yi iya kokarin ganin an cire wa kasar
miyagun takunkuman kariyar tattalin arizikin rashin adalci da Amurka ta dora wa kasar, sai dai ya kara
da cewa, ba za su taba mika wuya ba su watsar da muradun kasar a gaban kasashen ketare .
No comments