Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bayan Wata Hatsaniya, Kura Ta Lafa A Jihar Filato

  Daga Muhamamd A.Dalhatu  Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da cewar jami’an tsaro sun yi nasarar mayar da doka da oda a Yankin Gada Biyu dak...

 


Daga Muhamamd A.Dalhatu 

Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da cewar jami’an tsaro sun yi nasarar mayar da doka da oda a Yankin Gada Biyu dake birnin Jos sakamakon tashin hankalin da aka samu yammacin jiya wanda ya haifar da kone kone da kuma harbe-harben bindiga.

Wannan ya biyo bayan abin da ake dangantawa da yunkurin daukar fansa da wasu matasa suka yi sakamakon harin da aka kai karamar hukumar Bassa da ake zargin makiyaya akan Yan kabilar Irigwe abin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da kuma kona gidaje.

Harin na zuwa ne kwanakin bayan wani irin sa da aka kai karamar hukumar Riyom abin da ya sa majalisar tsaron jihar ta gudanar da taron gaggawa inda aka baiwa sojoji umurnin kara yawan jami’an su a yankunan kananan hukumomin da ake samun tashin hankalin.

Sanarwar da Daraktan yada labaran gwamnatin jihar Dr Makut Simon Macham ya rabawa manema labarai ta tabbatar da tura jami’an tsaron da kuma kwantar da tarzomar.

Macham ya ce matakin ya biyo bayan harin da aka kaiwa wasu motoci guda biyu da kuma cinna musu wuta lokacin da matasa suka tare babbar hanyar Gada Biyu.

Gwamnatin Jihar ta gargadi jama’ar jihar da su kaucewa daukar doka a hannun su wajen tare hanya suna kai hari akan matafiya.


No comments