Bom Ya Kashe 'Yan Shi'a A Pakistan A Yayin Juyayin Ashura

 


Akalla mutum uku suka mutu a yayin da wadansu 50 suka jikkata a wani harin bom da aka kai wa mabiya shi’a a yau Alhamis a kasar Pakistan a yayin juyayin Ashura.

Gwamnatin Pakistan ta tsaurara matakan tsaro a sassan kasar ta Pakistan mai rinjayen mabiya sunnah domin bayar da cikakken tsaro ga tsirarun mabiya Shi’a lokacin da su ke bukukuwan ranar Ashura a yau Alhamis kamar yadda Rfi Hausa ta labarto.

Babban jami’in tsaro na yankin da farmakin ya faru Kashif Hussain ya tabbatar da farmakin sai da ya ce har yanzu ba a gano masu hannu a harin ba, sai dai jami’an su na ci gaba da bincike domin gano nau’in abin fashewar da aka yi amfani da shi wajen kai farmakin.

Mabiya Shi’a kowacce shekara na amfani da ranar 10 ga watan Muharram domin tunawa da kisan gillar da aka yi wa Sayyadina Husseini jikan Fiyayyen halitta Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a filin Karbala a shekara ta 61 bayan Hijira.

Mabiya Shi’a suna da kashi 20 na yawan al’ummar Pakistan miliyan 220, inda a kowacce shekara suke gudanar da bukukuwa da jimamin rashin jikan fiyayyen halitta.


Post a Comment

0 Comments