A safiyar yau Asabar ne 21 ga watan Agustan 2021, masu kasuwanci a bakin titin Samarun Zariya, suka tashi da ganin wannan lamar...
A safiyar yau Asabar ne 21 ga watan Agustan 2021, masu kasuwanci a bakin titin Samarun Zariya, suka tashi da ganin wannan lamari na rushe musu shagunan da suke sana'a ba tare da sun kwashe komai na ciki ba.
Shi dai wannan rusau din an fara ne tun daga Makarantar Leather Research daura da Babban Gate din Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, inda ya nufi 'North Gate' har zuwa kasuwar Samaru, inda aka rushe duk wata Kwantena a gefen titi.
Wannan yasa wadanda abin ya shafa cikin alhini da tashin hankali, inda wasu ke ta kuka bisa hakan.
Bayanai sun tabbatar da cewa ma'aikatan dake kula da tsare-tsaren birni ta jihar Kaduna wato KASUPDA hade da rakiyar jami'an tsaro ne suka yi rusau din cikin daren jiya Juma'a 20 ga watan Agusta.
No comments