Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cikin Hawaye Messi Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Koma PSG

  Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Lionel Messi ya tabbatar da cewar yana gaf da kulla yarjejeniya da kungiyar PSG bayan ya sanar da kaw...

 


Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Lionel Messi ya tabbatar da cewar yana gaf da kulla yarjejeniya da kungiyar PSG bayan ya sanar da kawo karshen zaman sa a kungiyar Barcelona.

Yayin da yake ganawa da manema labarai cikin hawaye, Messi yace a wannan shekara shi da iyalan sa sun tabbatar da cewar zasu ci gaba da zama a Barcelona saboda abinda suke bukata kenan fiye da komai, bayan a shekarar da ta gabata ya nemi tafiya amma kungiyar ta hana shi.

A watan jiya Barcelona dake fama da dimbin bashi tace ta amince a tattaunawar da tayi da kaftin din nata domin kulla wata sabuwar kwangila ta shekaru 5 wadda ta kunshi rage albashin sa.

Messi yace lura da abinda ya faru, bai san abinda zai iya cewa ba, bayan zama sa na shekaru 21 a Barcelona yanzu zai bar garin tare da yaran sa guda 3 wadanda na farko Yan Barcelona ne sannan kuma  ‘yan kasar Argentina.

Dan wasan yace ya baiwa kungiyar Barcelona duk abinda take bukata daga wurin sa tun lokacin da ya rattaba hannu a kwangilar sa ta farko, kuma bai taba tunanin zai ga wannan ranar da zai yi sallama da ita ba.

Messi ya bayyana wannan lokaci a matsayin mai matukar wahala a gare shi, wanda bayan kwashe shekaru da dama da rayuwar sa a Barcelona, baya tunanin daukar irin wannan matakin da ya dauka a wannan rana na sallama da kungiyar da kuma birnin.

Dan wasan yace ya zuwa wannan lokaci babu wata yarjejeniyar da ya kulla da wata kungiya, duk da yake kungiyoyi da dama sun tuntube shi tun bayan sanarwar shirin barin Barcelona da kungiyar ta bayyana a ranar alhamis.

Rahotanni daga Jaridar Le Parisien dake Faransa na nuna cewar ana iya kammala tattaunawa tsakanin PSG da Messi yau lahadi domin kulla yarjejeniya.

Jaridar Daily L’Equipe tayi hasashen kulla kwangilar shekaru 3 tsakanin bangarorin biyu, abinda zai kai ga biyan Messi euro miliyan 40.


No comments