Sojojin Amurka da na Jamus
sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba a yau
Litinin a filin jirgin saman Kabul babban birnin Afghanistan, lamarin da yayi
sanadin mutuwar mutum 1 da jikkatar wasu 3kamar yadda RFI Hausa ta labarto.
Musayar wutar na zuwa ne a
daidai lokacin da Amurka tare da kawayenta ke kokarin hanzarta kwashe dubban
mutane daga Afganistan da suka hada da ‘yan kasarsu da wadanda suka yi aiki
tare a kasar, kafin kungiyar Taliban ta sake karbe iko.
A ranar Lahadin da ta
gabata ne dai rundunar sojan Amurka ta gargadi ‘yan kasarta da cewar su
kauracewa kusantar filin jiragen saman a birnin Kabul saboda yiwuwar fuskantar
barazanar tsaro.
Yanzu haka dai tirmitsitsin
masu neman tserewa daga Afghanistan na ci gaba da karuwa a wajen filin jragen
saman Kabul, a yayin da aka kwashe kimanin mutane dubu 30 daga kasar a
karkashin jagorancin Amurka, tun lokacin da Taliban ta kwace iko da birnin na
Kabul a ranar 15 ga Agusta.
'Yan Taliban, wadanda suka
yi kaurin suna wajen tsattsauran ra’ayi kan aiwatar da shari'ar Musulunci a
farkon mulkin su na tsakanin shekarun 1996 zuwa 2001, sun sha alwashin yin
sassauci a wannan karon.
0 Comments