Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki al'ummar Filato su rungumi zaman lafiya, tare da jaddada cewa gwamnatin na yin duk mai yiwuwa w...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
roki al'ummar Filato su rungumi zaman lafiya, tare da jaddada cewa gwamnatin na
yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen duk wani tashin hankali kamar
yadda Rfi Hausa.
Shugaban ya yi kiran ne a wata
sanarwa dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai,
Malam Garba Shehu, inda ya jaddada samun nasara tare da bukatar al’ummomin
yankin su hada kai don yakar bata gari, yana mai cewa tashin hankali ba zai
zama mafita ba.
Sanarwar ta ce duk da irin kokarin da gwamnati take yi wajen tabbatuwar zaman lafiya, bai kamata malaman addinai da sarakuna da sauran shugabannin al’umma su bari ana yada tashin hankali da tunzura jama’a ba.
Buhari ya ce akwai tarin matsalolin
da kasar ke fama a yanzu kuma yana da muhimmanci 'yan Najeriya da sauran
kasashe su fahimci kokarin da suke yi wajen kawar da duk wasu rigingimu a fadin
kasar.
Wannan na zuwa ne yayin da Gwamnan
Jihar Plateau Simon Bako Lalon ya ziyarci Yelwa Zangam inda aka kashe mutane
sama da 30 a makon jiya inda ya gana da Basaraken Yankin da kuma mutanen da
suka rasa Yan uwan su.
Bayan ziyarar mun tuntubi
kwamishinan yada labarai Dan Manjang kuma ga jawabin da yayi mana akai, kuna
iya latsa alamar sauti domin sauraren abin da yake cewa.
No comments