Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Gwarzo Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Daliban MAAUN 124 A Matakin Digiri Na Biyu

Shugaba kuma mu'assasin rukunin Jami'ar Maryam Abacha American University da Franco-British University, dake Kaduna, Far...Shugaba kuma mu'assasin rukunin Jami'ar Maryam Abacha American University da Franco-British University, dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo  ya bada tallafin karatu ga daliban Jami'ar ta MAAUN 124 su karanci bangaren jinya (Nursing) a matakin digiri na biyu. 


Wadanda suka ci wannan gajiyar na daga cikin daliban da suka zauna jarabawar kwararrun ma’aikatan jinya na shekarar 2020 kuma suka samu kyakkyawan sakamako. 


Farfesa Gwarzo ya bayyana tallafin karatun ne ga daliban a yayin taron cin abincin dare a ranar Laraba a Abuja wanda daliban suka shirya domin murnar nasarar da suka samu a yayin jarabawar.

A bayaninsa a matsayin Babban Bako na Musamman, Farfesa Abubakar Gwarzo ya ce shawarar ba su tallafin karatu domin ci gaba da karatunsu an yi ne bisa nasarar da suka samu a jarabawar kwararrun da suka rubuta.


Ya nuna matukar godiyarsa ga daliban bisa yadda suka sanya Jami'ar 'Maryam Abacha American University' ta yi alfahari da gagarumar nasarar da suka samu a jarabawar. "Don haka, ina farin cikin bayar da tallafin karatu ga kowanne ɗalibi cikin 124 domin yin karatun aikin jinya a matakin digiri na biyu domin na ƙarfafa ƙoƙarin ku da ƙara muku kwarin guiwa a karatun ku," in ji Farfesa Gwarzo.


Ya shawarci daliban da su zama masu hakuri tare da taimakon gajiyayyu a cikin al'umma, sannan ya kuma nemi da su zama jakadu na gari ga Jami'ar da suka kammala a duk inda suka tsinci kansu. 


Hukumar shirya jarabawar Unguwanzoma da aikin jinya ta Nijeriya, a ranar Talata 3 ga watan Agustan 2021, ta kaddamar da dalibai 294 wadanda suka samu nasarar cin jarabawar kwararru, inda a cikin su guda 124 sun kammala karatunsu ne a Jami'ar Maryam Abacha American University dake Jamhuriyyar kasar Nijer. 

Taron ya gudana ne a dakin taro na 'Officers' Mess & Suites' dake Hedikwatar Sojin sama ta Nijeriya (NAF) a Kado, Abuja.

No comments