Shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a Nijeriya sun mika wasu mutane 11 da ake zargin cewar masu garkuwa da mutane ga run...
Shugabannin
kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a Nijeriya sun mika wasu mutane 11 da
ake zargin cewar masu garkuwa da mutane ga rundunar ‘yan Sandan Jihar Taraba.
Shugaban
kungiyar Sahabi Tukur ya bayyana cewar sun yi hakan ne sakamakon alkawarin da
suka yiwa Sarkin Muri Abbas Tafida na tona asirin wadanda ke aikata irin wannan
laifi a cikin su.
Tukur
ya ce sun kafa wani kwamiti a tsakanin su da ya kunshi bangarorin Fulanin dake
Jihar da za su yi aiki da ‘yan sanda a kananan hukumomi 16 domin zakulo masu
garkuwa da mutane da kuma aikata wasu laifuffuka.
Kwamishinan
‘yan Sandan Jihar Abimbola Sokoya ya yaba da matakin da kungiyar ta dauka na
shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin.
Sokoya
ya kuma bukaci samun hadin kai tsakanin Jihohin Adamawa da Binuwe da kuma
Taraba domin dakile ayyukan garkuwa da mutane da wasu laifuffukan da suka
addabi jama’a, yayin da ya sha alwashin bai wa Fulanin goyan bayan samun
nasara.
Wasu
masu garkuwa da mutane guda 6 da suka tuba a wurin, an ba su Alkur’ani sun
rantse cewar ba za su aikata laifin ba ko kuma satar shannun jama’a.
A
watannin da suka gabata Sarkin Muri Abbas Tafida ya sha alwashin daukar mataki
mai tsauri na kashe ‘yan’uwan mutanen da suka addabe su wajen garkuwa da mutane
ko satar shanu ko kuma kashe jama’a a yankin kamar yadda Rfi Hausa ta labarto.
No comments