Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gidauniyar Farfesa Gwarzo Ta Bada Tallafin Motar Naira Miliyan 50 Ga Jami’ar Al-Istiqama

  Shugaban Jami'ar Maryam Abacha na Nijeriya (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ba da kyautar motar bas mai kujeru 66 mai wacce f...

 


Shugaban Jami'ar Maryam Abacha na Nijeriya (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ba da kyautar motar bas mai kujeru 66 mai wacce farashinta ya kai Naira miliyan 50 ga Jami'ar Al-Istiqama Sumaila a jihar Kano.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda har wala yau shi ne Shugaban Ƙungiyar Jami'o'i Masu zaman kansu ta Afirka (AAPU), har wala yau ya aza harsashin ginin dakunan kwanan dalibai wanda ya kai girman dakuna 160 wanda aka sanya ma sunansa a Jami'ar.

Da yake gabatar da Motar Bas din na alfarma ga Shugaban Jami’ar Al-Istiqama, Honorabul Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila a Harabar makarantar da ke Sumaila a ranar Lahadi, Farfesa Gwarzo ya ce Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar ce ta bayar da Bas din ga Jami’ar.

Ya ce wannan karamcin an yi shi ne domin inganta ayyukan ilimi a sabuwar Jami'ar da aka kafa, saboda a cewarsa sufuri na daya daga cikin muhimman bangaren da ke da bukatar kulawa da bada tallafi. 

Farfesa Gwarzo har wala yau ya ce; “Al-Istiqama da Jami’ar Maryam Abacha ta Nijeriya tamkar tagwaye ne, saboda haka, dole ne su taimaki juna. MAAUN a shirye take a koyaushe ta taimaki Al-Istiqama a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya ci gaba da cewa; “Da farko, wanda ya kafa Jami’ar ya so ya kafa Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya ne, amma da ya tuntube ni, sai na shawarce shi akan ya fadada shirinsa domin ya kafa Jami’a kuma ga mu a yau wannan burin namu ya tabbata. 

Sannan ya kara da cewa; “Mutanen Sumaila da jihar Kano baki daya akwai bukatar su godewa Honorabul Sumaila saboda hangen nesan da ya yi. Wannan gagarumin aikin ba Kawu Sumaila kadai ne zai amfana da shi ba,  al’ummar Sumaila, Kano da Nijeriya baki daya sune ma za su amfana. Wanda ya kafa wannan Jami’ar tabbas ya tabbatar da cewa shi mai kishin ƙasa ne na gaskiya.

Farfesa Gwarzo, har wala yau ya mika godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki da ya sanya aka cimma nasarar kafa Jami’ar, inda ya ce “Allah ne kaɗai ne zai iya ba Honorabul Sumaila ladan kyakkyawan aikin da ya ke yi wa Ɗan Adam. Makarantar za ta amfani jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya”, ya tabbatar. 

A na shi jawabin, Shugaban Jami’ar Al-Istiqama, Honorabul Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila, ya ce za a kammala Dakunan kwanan Daliban mai dauke da dakuna 160 nan da shekara mai zuwa.

Sumaila ya yi bayanin cewa ana gina dakunan kwanan dalibai din ne domin su dace da wadanda ake da su, yana mai cewa Jami’ar ta samar da manyan dakunan kwanan dalibai biyu ga dalibai mata da maza.

"Mun riga mun shigar da Dalibai 400 domin karantar kwasa-kwasai daban-daban sannan wasu guda 100 na jarabawar shiga makarantun gaba da Sakandare (IJMB)," in ji shi.

Ya kara da cewa an radawa Dakunan kwanan dalibai sunan Farfesa Gwarzo ne saboda gagarumar gudummawar da yake bayar wa a bangaren ilimi da ‘yan Adamtaka, yana mai cewa "mun karrama Gwarzo ne ba saboda dangantakar da muke da ita da shi ba, sai domin gudummawar da yake bai wa bangaren ilimi da matasa."


No comments