Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Matawallen Maradun Ya Amshi Katin Zama Dan Jam’iyyar APC A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim, Funtua A yau Laraba, Gwamna Muhammad Bello Matawalle Maradun ya amshi katin zama dan Jam’iyyar APC a mazabarsa da ke ...


Daga Hussaini Ibrahim, Funtua

A yau Laraba, Gwamna Muhammad Bello Matawalle Maradun ya amshi katin zama dan Jam’iyyar APC a mazabarsa da ke Kanwuyi cikin karamar hukumar Maradun jihar Zamfara.

Gwamna Muhammad Matawalle ya bayyana cewa, wannan rana ita ce ranar hadin kai ga 'yan jam’iyyar APC na jihar Zamfara baki daya. “‘Yan jam’iyyar mu mu zamo tsintsiya madaurin ki daya, babu bambancin tsakaninmu a wajen tafiyar da jam’iyya ga kowa da kowa. Fatan mu shi ne samun nasarar kawo zaman lafiya da ci gaban jihar Zamfara”, ya tabbatar.

A na shi jawabin, wakilin uwar Jam’iyya na  amsar katin jam’iyyar APC na kasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya bayyana cewa, sun zo ne domin ganin an gudanar da amsar katin jam’iyyar APC ga kowa da kowa domin samun nasara bin shugabani jam’iyyar na gunduma da na kananan hukumoni da na jihar da za su wakilci su a zaben zhugabanin jam’iyyar na kasa; “Fatanmu shi ne mu ga al'ummar jihar Zamfara sun shigo jam’iyyar APC gaba daya domin cin moriyar mulkin adalci a karkashin jamiyyar APC”.


No comments