Gwamnati Ta Daina Daukar Wayarmu, Za Mu Tsunduma Yajin Aiki, Inji ASUU


Kungiyar malaman jami'o'in Nijeriya, ASUU ta bayyana cewa a shirye take ta sake shiga wani sabon yajin aiki kan abin da ta kira gazawar gwamnati wajen cika alkawuran da aka cimma da ita.

Kungiyar ta bai wa gwamnati wa'adi zuwa gobe Talata ta tuntube su ko koma ta soma yajin aiki.

Shugaban ASUUn, Farfesa Emmanuel Osodeke a tattaunawarsa da jaridar The PUNCH ta Nijeriya ya ce gwamnati ta daina daukan wayarsu.


Post a Comment

0 Comments