Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cutar Kwalara Ta Kashe Mutum 23 A Jihar Sakkwato

  Gwamnatin Jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar mutane 23 sakamakon barkewar cutar kwalara ko amai da gudawa a jihar. Kwamishinan lafiya A...

 


Gwamnatin Jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar mutane 23 sakamakon barkewar cutar kwalara ko amai da gudawa a jihar.

Kwamishinan lafiya Ali Inname ya bayyana haka ga manema labarai, inda yake cewa cutar ta yadu zuwa kananan hukumomi 13 daga cikin 23 da ake dasu.

Inname ya danganta matsalar da rashin tsafta musamman bayan gari a bainar jama’a abinda ke gurbata ruwan shan da jama’a ke amfani da shi a lokacin damina.

Ko a watan Maris da ta gabata, sanda gwamnatin jihar ta rufe kwalejin ‘Yam mata dake Mabera saboda samun cutar wadda ta kama dalibai akalla 70.

Cutar kwalara na daga cikin cututtukan dake hallaka jama’a a Najeriya kowacce shekara, inda a watanni 6 na farko wannan shekarar aka samu mutuwar mutane sama da 300 a jihohin kasar da aka samu barkewar ta kamar yadda Rfi Hausa ta labarto. 


No comments