Gwamnatin Nijeriya Ta Gaza Wajen Samar Wa Jama’a Tsaron Da Ya Kamata- Amnesty


Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana takaicin ta game da gazawar gwamnatin Tarayyar Nijeriya na samar wa jama’ar kasar tsaron da ya kamata. 

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoto da ta fitar, game da yanayin da tsaro ke ciki a Nijeriyar.

A cewar Amnesty International cikin wata guda kawai an kashe mutane 112 a rikice-rikicen da aka samu a jihohin Kaduna da Filato a Nijeriyar.

Kungiyar cikin rahoton da ta fitar ta ce baya ga mutanen da suka hallaka dalilin rikice-rikicen, masu garkuwa da mutane sun kuma sace wasu 160.

Amnesty din ta kuma kara da cewa an kuma samu tashin rikici tsakanin Fulani da makiyaya da ya lashe rayukan mutane da dama.

Kungiyar ta kare hakkin dan Adam ta kuma ce da alama gwamnatin Najeriya bata wani yunkuri na tabbatar da tsaro a kasar, la’akari da yadda ake sace mutane baji ba gani, yayin da ‘yan ta’adda ke kaiwa kauyuka hare-hare kusan kullum da kuma kisan kan mai uwa da wabi.

Rahoton na Amnesty ya kuma jadadda cewa akalla mutane 78 aka kashe yayin da aka yi garkuwa da 160 tsakanin 3 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta a jihar Kaduna cikin su kuma har da 121 na makarantar Bethel Baptist.

A jihar Plateau kuma mutane 34 aka kashe 7 daga cikin su makiyaya a ranar 1 ga watan Yuli a garin Dogon Gaba sai Fulani biyu da aka kashe a kauyen Fusa lokacin da suke kan hanyar su ta neman shanun su da suka bata.Post a Comment

0 Comments