Gwamnatin Zamfara Ta Ceto Dalibai 17 Na Kwalejin Aikin Gona Da Ke Bakura


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta amso Daliban Kwalejin Aikin Gona da Malamansu 17 sakamakon sulhu da aka yi da su. 'Yan bindigar sun kashe mutum biyu daga cikin su.

Gwamna Matawalle ya jinjinawa Rundunar 'Yan sandan jihar wanda da kokarinta ne aka amso su bayan sun kwashe kwanaki sha biyar a hannun 'yan bindigar.

Kwamishinan 'Yan sanda Ayuba Elkana ya bayyana cewa, da karfafawar Gwamna Matawalle a gare su ya sanya suka samu nasarar ceto daliban. 

Post a Comment

0 Comments