Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hanyoyin Kariya Daga Cutar Kwalara Daga Dr. Najeeb Maigatari

  Cutar Amai da gudawa (Cholera) yanzu haka ta na addabar wasu sassa na Arewacin Najeriya, musamman jihohin Jigawa, Yobe, Kano, inda aqall...

 


Cutar Amai da gudawa (Cholera) yanzu haka ta na addabar wasu sassa na Arewacin Najeriya, musamman jihohin Jigawa, Yobe, Kano, inda aqalla  ta yi ajalin daruruwan mutane zuwa yanzu.

Bisa rahoton Hukumar Yaqi da Daqile Cututtuka masu yaduwa (NCDC) zuwa ranar 25 ga watan da ya gabata, cutar ta yi ajalin mutane 653 a jihohi 23 (har Abuja kenan) daga cikin 36(+1) da ake da su a Najeriya, inda kuma fiye da mutane dubu 27 su ka kamu da ita.

Me ke Kawo Cutar Amai da Gudawa?

- Wata kwayar cutar bakteriya mai suna ‘Vibrio Cholerae’ ke kawo cutar.

Ta Ya Ake Daukar Cutar?

- Cin Abinci/Abin sha wanda ya gurbata da wannan kwayar cutar (vibrio cholerae).

- Rashin tsaftace hannu, kayan cin abinci/sha wanda akwai kwayar cutar akan su, da ire-iren su.

- [Sauran bayanai a kasa].

Alamomin Cutar:

- Fara Amai da gudawa nan da nan, cikin qanqanin lokaci.

- Gudawar ta na da wani kala na musamman: kamar ruwan shinkafa.

- Sauran Alamomi sun danganci karancin ruwa a jiki (kamar fadawar idanu, bushewar baki dss), da kuma rashin daidaiton sinadaran ‘electrolytes’ da ke cikin jini (kamar makuwa, jijjiga, ciwon ciki mai tsanani dss).

Ya Ake Tabbatar Da Ita?

- Daga Alamun da aka lissafa a sama (gudawar cutar Cholera ta bambanta da saura ta kalar ruwan shinkafa da ta ke da shi).

- Tabbatar da samuwar kwayar cutar ‘vibrio Cholerae’ a cikin gudawar mutum (idan an gwada a Laboratory kenan, ba da ido ba).

Ya Ake Magance Ta?

- A gaggauta zuwa Asibiti shi ne babban taimakon da za’a iya yiwa mutum.

- Ana iya hada ruwan gishiri da suga (ORS) a ba mutum a matsayin taimakon gaggawa kafin a tafi da shi Asibiti (amma wannan bai dauke wajibcin zuwa Asibiti ba), pls!

Hanyoyin Kariya:

- Mafi muhimmanci: tsaftar abinci/Abin sha; da kuma tabbatar da an dafa abinci ya dahu sosai.

- Wanke hannu akai-akai don tabbatar da ba ya dauke da kwayar cutar, musamman kafin cin abinci/abin sha.

- Ya na da matuqar muhimmanci ake wankewa yara hannu duk lokacin da su ka gama wasa.

- Wanke kayan lambu da na marmari (vegetables and fruits) sosai, kafin a yi amfani da su.

- KULA DA TSAFTAR BANDAKI (mafi akasari a cikin bahaya kwayar cutar ke fita, sai sauran al’umma su dauka ta hanyar gurbataccen abinci/abin sha).

- Wayar ma da al’umma kai akan illar yin bahaya a waje (open defecation) musamman wadanda ke karkara.

- Tabbatar da ‘chlorinating’ ruwa daga magudanai (aikin hukuma).

- A gida, mutum zai ke iya tafasa ruwa, idan ya huce sai ya sha, idan ya na zargin ruwan zai iya zama gurbatacce.

- Da sauran tsaftar muhalli, gida dss.

- Akwai rigakafin cutar da ake yi, amma zuwa yanzu ba ta da wani inganci na azo a gani, ta na bada kariya ne na wucin gadi kawai.

Kar a manta: A GAGGAUTA ZUWA DA MUTUM ASIBITI DA ZARAR YA KAMU!


No comments