Hisbah A Kano Ta Cafke Sadiya Haruna Bisa Yada Hotunan Batsa

 


Hukumar Hisbah ta Kano ta cafke fitacciyar mai tattaunawa lamarun kayan mata da magungunan mata a shafukan sada zumunta, wato Sadiya Haruna bisa yada bidiyon tsiraici.

A cewar majiyarmu, an cafke Sadiya Haruna a jiya ne, kuma za a gurfanar da ita gaban kotun shari’ar Musulunci a Kano domin ta fuskanci hukunci bisa dokokin shari’ar Musulunci.

Babu cikakken bayani dangane da kamun na ta har ya zuwa hada rahoton nan.


Post a Comment

0 Comments