Hujjojin Da Aka Gabatar Sun Yi Tsauri Na Yanke Hukunci Nan Take, Inji Alkalin Da Ke Shari'ar Abduljabbar

 


Daga Muhammad A. Dalhatu

-An Ɗage Sauraron Ƙarar Abduljabbar Kabara Zuwa 2 Ga Satumba


Kotu a jihar Kano ta ɗage sauraron ƙarar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara zuwa 2 ga Satumban 2021.

A ranar Laraba ne Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ɗage sauraron ƙarar bayan da aka yi zama na biyu tun fara shari'ar a birnin Kano.

Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar Malam Abduljabbar kan zarginsa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, zargin da Shaikh Abduljabbar ya sha musantawa.

Mai Shari'a Sarki Yola ya ce ya ɗage sauraron ƙarar ne saboda duk hujjojin da aka gabatar sun yi masa tsauri ya yanke hukunci nan take.

Ya ƙara da cewa akwai bukatar ya sake duba su, sannan ya san matsayar da zai ɗauka kan sabbin tuhume-tuhumen da gwamnati ta gabatar a zaman kotun na yau kan Sheikh Abduljabbar, ku kuma mafani da tuhume-tuhumen farko da aka gabatar.

Lauyoyin gwamnati sun buƙaci a ba su dama su karanto sabbin tuhume-tuhumen da suka je da su a kan Sheikh Abduljabbar, amma nasa lauyoyin suka soki hakan.

Lauyoyin Abduljabbar sun ƙalubalanci takardar sabbin tuhume-tuhumen da lauyoiyin gwamnati suka gabatar.

BBC sun labarto cewa; Barista Saleh Bakaro wanda shi ne lauyan da yake jagorantar ɓangaren Abduljabbar, ya ce gaba daya lauyoyin SAN din da gwamnati ta dauko ba su da hurumi a tsarin dokar aikin lauya na shiga zuwa ƙaramar kotu.

"Daga babbar Kotun Tarayya ne aka yarda SAN su fara zuwa kotu. Sannan sabbin tuhume-tuhumen da suka bayar ya saɓa da tsarin dokar shari'ar Musulunci.

"Ba a yarda mutum ya sake shigar da tuhuma ko ƙara kan wata da ake saurara ba, bayan gabatar da shaidar farko a tsarin dokar Shari'ar Musulunci," a cewar Bakaro.

Su kuwa lauyoyin ɓangaren gwamnati sun ce kamata ya yi lauyoyin Abduljabbar su dakata a gama karanto sabbin tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda ake ƙarar kafin su kawo wata suka kan lamarin.

Sun ce a bisa doka wajibi ne a karanto cajin wanda idan an kammala ne sannan wani bangare zai iya suka ko goyon bayan a ci gaba da shari'a.

Barista Surajo Sa'ida SAN mai jagorantar lauyoyin gwamnati ya dogara ne da Sashe na 390 ƙaramin sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda a don haka ya buƙaci lauyan Abduljabbar ya janye sukar da ya yi har sai bayan an kammala karanto sabbin tuhume-tuhumen da suka gabatar wa kotu.

Lauyoyin Abduljabbar sun ce sashen da lauyoyin gwamnati suka dogara da shi, na magana ne kan cajin da aka gabatar tun ranar farko da aka gabatar da Abduljabbar a kotun ranar 16 ga watan Yunin da ya gabata.

A ranar fara sauraron ƙarar an karanta masa tuhumar da ake masa ne ta farko ta 'yan sanda, wanda kuma bai amsa aikata laifin ba, don haka ya riga ya amsa ƙara, wanda hakan ke nuni da an fara shari'a.

Don haka a cewarsu sashe na 390 da lauyoyin gwamnati suka gabatar ba shi da hurumi a wannan shari'a da ake yi, in ji Bakaro.

To bayan ɗaukar lokaci yana rubuce-rubuce ne sai Alkai Sarki Yola ya ce yana bukatar karin lokaci don sakae nazartar tuhume-tuhumen da kuma hujjojin da bangarorin biyu suka gabatar masa.

Ya ce zai yi hana ne "don kare mutuncina da darajar aikina, da kuma adalcin da aikina ya buƙace ni da yi," in ji shi.

Daga hakan ne kuma ya bayar da zabin ranaku uku na 1 ko 2 ko 6 ga watan Satumban 2021 a matsayin ranar komawa kotu, inda aka ƙarshe aka zaɓi 2 ga watan Satumban.


Post a Comment

0 Comments