Sanata Bala Ibn Na'Allah, ɗan majalisar Dattawan Nijeriya daga jihar Kebbi, wanda ake zargin wasu batagari da kashe babban ɗansa, Abdu...
Sanata
Bala Ibn Na'Allah, ɗan majalisar Dattawan Nijeriya daga jihar Kebbi, wanda ake
zargin wasu batagari da kashe babban ɗansa, Abdulkareem a gidansa da ke Malali
a Kaduna, ya ce yana fatan mutuwar ɗan shi ya kawo karshen matsalolin tsaron Nijeriya.
Sanatan
ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar wanda ya ce ran ɗansa bai fi na
kowanne ɗan Nijeriya ba.
Ya
ce: "Maharan sun kutsa gidan ɗana ta rufin kwano suka makure shi har ya
mutu. Ni da iyalina ba za mu manta da wannan rashi ba kuma za mu ci gaba da
masa addu'a, saboda mutumin kirki ne".
Sanata
Na'Allah da ke wakiltar Kebbi ta Kudu shi ne shugaban kwamitin harkokin sojin
sama a majalisar dattawa, kuma baya ƙasar lokacin da aka kashe ɗan nasa kuma
wadanda suka kashe shi ba sa dauke da bindiga.
A
jiya ne dai aka samu rahotan hallaka ɗan sanatan mai shekara 36 a gidansa da ke
titin Umar Gwandu a Malali na jihar Kaduna.
Ƴan
sanda sun ce maharan sun tsere da motarsa kirar Lexus SUV bayan hallaka shi.
No comments