Jami'ar Al-Istiqama Za Ta Gina Dakunan Kwanan Dalibai 160 Da Sunan Farfesa Adamu GwarzoHukumar gudanarwa ta Jami'ar Al-Istiqama dake Sumaila a jihar Kano, ta kammala shiri tsaf domin gina dakunan kwanan dalibai maza 160 a cikin jami'ar domin ta sanya sunan shugaba kuma mu'assasin Jami'ar Maryam Abacha American University (MAAUN) ta Jamhuriyyar Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo. 

Tuni Jami'ar ta nemi Farfesa Abubakar Gwarzo da ya sanya ranar da ta dace domin taron kaddamar da ginin kwanan dalibai maza 160 da sunan Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.  


Takardar neman na dauke ne da kwanan watan 10 ga watan Agustan 2021 wanda mu'assasin Jami'ar Al-Istiqama, Honorabul Sulaiman A. Kawu Sumaila ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Laraba. 


A cewar wasikar, kudurin Jami’ar na sanyawa dakunan kwanan dalibai sunan Farfesa Abubakar Gwarzo ya yi la'akari ne da irin goyon bayan da yake bayarwa, nuna karamci, fahimta da kuma jajircewarsa ga bangaren ilimi da ci gaban Dan Adam baki daya.

"dangane da abin da aka ambata a sama, tare da gudummawarka ga Jami'ar Al-Istiqama, Sumaila, da kuma nasarar da ka samu a bangaren ilimin Jami'a, muna neman ka amshi wannan karramawar tare da sanya ranar da ta dace domin wannan taro mai tarihi", inji wasikar. 

Ya kara da cewa, wannan aikin yana daga cikin wani bangare na kokarin Jami'ar na samar wa da dalibanta ingantacce kuma amintaccen muhalli domin gudanar da aiki yadda ya kamata. 


"Da fatan za a dubi wannan girmamawa na wanda ya kafa Jami’ar da al'ummar Jami'ar baki daya, ”in ji Jagora/Mu'assasin Jami'ar Al-Istiqama. 

Post a Comment

0 Comments