Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Jami'ar MAAUN ta Taya Sabon Shugaban Jami'ar Dan Dikko Dan Koulodo, Farfesa Mamane Sani Murna

Wanda ya kafa kuma shugaban Jami'ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya sabon shugaban ...


Wanda ya kafa kuma shugaban Jami'ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya sabon shugaban Jami'ar Maradi dake Jamhuriyyar kasar Nijer, Farfesa Mamane Sani da mataimakinsa, Dr Adamou Saidou murna. 


Sakon murnar na cikin wasikar da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Laraba a Kano. 

A cewar Farfesa Abubakar Gwarzo, nada Farfesa Mamane Sani a matsayin sabon shugaban Jami'ar ya dace, idan aka yi duba da irin gudummawar da ya bai wa bangaren ilimi a Jamhuriyyar kasar Nijer. 

Shugabam Jami'ar ta MAAUN, ya yi fatan cewa sabon shugaban Jami'ar zai kawo ci gaban da ya kamata ga Jami'ar ta Dan Dikko Dan Koulodo. 

Sannan ya yi nuni da cewa nadin sabon shugaban Jami'ar ta Maradi zai kara wa Jami'ar daraja da inganci a sassan duniya. 

"A madadin hukumar gudanarwa ta MAAUN, ina son taya ka murna bisa nadin da aka yi maka a matsayin sabon shugaban Jami'ar", inji Farfesa Abubakar Gwarzo. 

A karshe, ya yi addu'ar Allah ta'ala ya bai wa sabbin shugabannin kwarin guiwa da hikima wajen daukaka darajar Jami'ar. 

No comments