Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami'ar MAAUN Ta Yi Alhinin Rasuwar Dalibinta Tanimu Darma

Shugaba kuma mu'assasin Jami'ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, dake Kadun...Shugaba kuma mu'assasin Jami'ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika sakon ta'aziyyah ga iyalan daya daga cikin daliban Jami'ar, Alhaji Tanimu Sule Darma Kaduna wanda ya rasu a kwanakin nan. 

Marigayin dalibi ne a sashen lafiyar al'umma a Jami'ar MAAUN dake Jamhuriyyar kasar Nijer, ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya. 


Sakon ta'aziyyar yana dauke ne a sanarwar da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Talata. 

Ya bayyana rasuwar Tanimu Darma a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalinsa ba amma ga dukkanin ma'aikatan jami'ar baki daya. 

Shugaban MAAUN din ya kuma bayyana mamacin a matsayin dan kishin kasa, wanda ya yi aiki tukuru wajen ci gaban al'ummarsa ta Kawo dake Kaduna ta hanyar samar da dakin magani mai zaman kansa a yankin Sabon Kawo. 

A cewar Farfesa Abubakar Gwarzo, Marigayin har wala yau ya bayar da gudummawa wajen samar wa da daliban da suka cancanta daga jiharsa damar karatu kyauta a Jami'ar ta MAAUN. 

"A madadin hukumar gudanarwa ta Maryam Abacha American University (MAAUN), ina son mika sakon ta'aziyyah ga iyalai, 'yan'uwa da abokan Tanimu Darma bisa rasuwarsa", inji shi. 


"Allah ta'ala ya sanya shi a Aljannah Firdaus, ya kuma bai wa iyalinsa hakurin jure rashinsa da suka yi," inji Farfesa Abubabar Gwarzo. 

No comments