Daga Ammar M. Rajab Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a ranar Alhamis ya bayyana damuwarsa bisa matsalar tsaron da yake addabar ...
Daga Ammar M.
Rajab
Gwamnan jihar
Katsina, Aminu Bello Masari a ranar Alhamis ya bayyana damuwarsa bisa matsalar
tsaron da yake addabar jiharsa, inda ya tabbatar da cewa akalla kananan
hukumomi 10 cikin 34 da ake da su a jihar, suna fama da hare-haren ‘yan bindiga
da masu garkuwa da jama’a.
Ya tabbatar da
cewa tabarbarewar ta’addancin ‘yan bindiga, masu garkuwa da jama’a, fyade da
fashi da makami sun toshe duk wani kokarin gwamnati wajen tabbatar da zaman
lafiya a jihar.
Masari, ya
bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin Shugaban Hafsan sojojin Nijeriya,
Laftanar Janar Faruk Yahayaa gidan gwamnatin Katsina, inda ya nemi al’umma da
hukumomin tsaro da su yi aiki tare wajen yaki da ayyukan ‘yan bindiga, masu
garkuwa da jama’a da sauran batagari da suke jihar.
Ya ci gaba da
cewa sojoji da sauran hukumomin tsaro
suna da bukatar kayan aiki da goyo baya wajen dakile ayyukan ‘yan bindiga da
sauran matsalolin tsaro da yake addabar kasarnan, inda ya kara da cewa; yanzu
duniya ta koma zamanin fasaha, domin haka; “ta hanyar fasaha, za ku iya yakin
ku da jami’ai kalilan”.
Ya ce; “mu a nan
Katsina, idan muka ce muna cikin farin ciki, ba mu fadi gaskiya ba. Muna cikin
damuwa dangane da batun harin ‘yan bindiga da ya hada da garkuwa da jama’a, yi
wa mata fyade wadanda ba su ji ba ba su gani ba, fashi da makami a manyan
tituna. Ina son a yi amfani da fasaha
yadda ya kamata wajen kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga.
“Ba muna yaudarar kanmu ba ne na cewa za mu
kawar da aikata laifi; ba a taba yin haka ba a baya, kuma ba za a yi shi a yau
ba ko a gobe, amma zamu iya dakile shi ta yadda ba zai addabi rayuwar al’ummar
ba kamar yadda yake faruwa a yau”, inji shi.
Masari ya ci gaba
da cewa; “10 cikin 34 na kananan hukumomin jihar Katsina, duk suna karkashin
munanan hare-haren ‘yan bindiga a kowacce rana. A don haka, da wannan a ranmu,
babu dalilin da zai sanya mu bacci. Wayarmu
a koyaushe tana kunne domin mu rika jin me yake faruwa a wadannan kananan
hukumomi. Kafin karin kumallon safe, an gaya min abin da ya faru da daddare. A takaice,
ba ma jindadin yanayin da muke ciki, amma mungodewa Allah”.
Domin dakile
matsalar, ya ce, gwamnatin jihar ta yi wa dokokin kananan hukumomi garambawul
sannan ta samar da tsarin tsaro na mataki uku a jihar domin dawo da matsayin Sarakunan
Gargajiya, addini, shugabancin matasa da mata wajen yaki da rashin tsaro a fadin
jihar.
Tun da farko, Shugaban
Hafsan sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Yahaya, ya shaida wa gwamnan cewa yana
jihar Katsina a wani ziyarar aiki domin duba rundunonin soji a karkashin
runduna ta 8 ta sojojin Nijeriya, inda ya sha alwashin yin aiki tare da sauran ‘yan’uwansa
hukumomin tsaro domin dakile rashin tsaro a jihar.
No comments