Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da masu kiran cewar mutane su tanadi makamai domin kare kan su daga hare haren da ‘yan bindiga ke kai mus...
Gwamnatin
Nijeriya ta yi watsi da masu kiran cewar mutane su tanadi makamai domin kare
kan su daga hare haren da ‘yan bindiga ke kai musu ba tare da kaukautawa ba.
Ministan
‘yan Sandan kasar Muhammad Dingyadi ne ya bayyana hakan, bayan kiran da
Gwamnonin Katsina da Binuwe suka yi wa jama’ar su cewar su nemi makamai domin
kare kan su daga wadannan mahara.
Dingyadi
ya ce saboda ‘yancin da ake da shi a Nijeriya kowa na da hurumin bayyana
ra’ayinsa, amma abin sani shi ne jami’an tsaro suna iya bakin kokarin su, kuma
abin da ake bukata daga jihohi shi ne samar da jami’an tsaron Anguwanni da za su
taimaka musu.
Ministan
ya ce sojoji da ‘yan Sandan dake aiki domin kare lafiyar jama’ar kasar na
bukatar goyan bayan kowanne dan kasa na gari, yayin da ake bukatar mutane su
dinga sa ido akan abin da ke faruwa a yankunan su suna kuma shaidawa jami’an
tsaro domin daukar mataki kamar yadda rahoton RFI Hausa ya tabbatar.
Ganin
yadda karuwar hare hare da ‘yan bindiga ke kai wa suna hallaka rayukan jama’a
da kuma sace dukiyoyi ba tare da kaukautawa ba, ya sa jama’a korafi game da
rawar da gwamnati ke takawa wajen kare lafiyar su.
Jihar
Katsina da Zamfara da Binuwe na daga cikin wadanda ke fuskantar irin wadannan
hare hare, abin da ya sa gwamnonin su fusata da kuma umurnin jama’a da su kare
kan su.
Gwamnan
Katsina Aminu Bello Masari ya ce gara mutane su sayi makamai maimakon biyan
kudin fansa.
No comments