Kofin Aisha Buhari: Za A Fafata Tsakanin Falcons Da Morocco

 


Tawagar Super Falcons ta Najeriya zata duka wasa da Morocco a wasan farko na neman cin kofin Dakta Aisha Buhari, wato uwargidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan da kungiyoyin biyu suka kasance a rukuni daya wato A.

A yayin wani katsaitattaccen buki da aka gudanar a Eko Hotel na birnin Lagos ranar Laraba wanda ya samu halartan manyan mutane da fitattun ‘yan wasa aka fitar da jadawalin gasar da tawagar mata daga kasashen Afirka 6 zasu hallara a birnin Lagos.

Rukunin A:

Akwai Najeriya mai masaukin baki da Morocco da kuma Mali.

Sai kuma Rukunin B:

Dauke da Kamaru da Ghana da kuma Afirka ta Kudu.

Wasan farko da Super falcons zata kara da Morocco  zai gudana a filin wasa na Mobolaji Johnson a Onikan dake Legas, ranar 13 ga watan Satumba.

Gasar wasannin kwallon kafar mata ta neman cin kofin Dakta Aisha Buhari wanda shine irinsa na farko zai gudana ne tsakanin ranakun 13 ga zuwa 21 ga watan Satumba mai zuwa.

Post a Comment

0 Comments