Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu ta dakatar da 'Kama Sunday Igboho Ko Rufe Asusun Bankinsa'

  Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke kudancin Nijeriya ba ta amince da buƙatar 'yan sandan farin kaya (DSS) da ministan shari'ar Naje...

 


Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke kudancin Nijeriya ba ta amince da buƙatar 'yan sandan farin kaya (DSS) da ministan shari'ar Najeriya ba ta kama mai fafutikar kafa Ƙasar Yarabawa mai suna Sunday Adeyemo, a cewar rahoton Channels TV kuma BBC Hausa ta nakalto.

Kazalika, kotun ta dakatar da DSS da Ministan Shari'a Abubakar Malami daga tilastawa ko kuma rufe asusun banki na Mista Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

Channels ta ruwaito Mai Shari'a Akintola yana bayar da umarnin bayan lauyan Igboho, Yomi Aliu (SAN), ya gabatar da buƙatar hakan.

Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, Mista Aliu ya ce "kotun ta bayar da umarnin kar a kama shi [Igboho] ko tsare shi ko kashe shi a cikin kwana 14 masu zuwa".

Umarnin kotun na zuwa ne a ranar da DSS ɗin ta gurfanar da mabiyan Igboho 12 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Ana zargin mabiyan nasa ne da "tara makamai da nufin haddasa tashin hankali a Najeriya".

A gefe guda kuma, wata kotu a ƙasar Benin na tuhumar Sunday Igboho da sabbin laifuka da suka haɗa da shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba da haɗa baki da jami'an shige da fice da kuma yunƙurin haddasa yamutsi.

Jami'an tsaron Benin sun kama shi ne yayin da yake yunƙurin tafiya Jamus jim kaɗan bayan ya fice daga ƙasarsa Najeriya wadda ke zargin sa da haddasa fitina da kuma yunƙurin raba ƙasar.

No comments