VOA
Hausa ta labarto cew; wata kotu a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin
Najeriya, ta hana Uche Secondus ya rika ayyana kansa a matsayin shugaban
jam’iyyar PDP.
Matakin
kotun na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddamar cikin a babbar jam’iyyar adawar
ta PDP inda wasu jigajigan jam’iyyar ke neman Secondus ya sauka da mukaminsa
yayin da shi kuma ya yi kememe ya ki sauka.
A
ranar Litinin Mai Alkali O. Gbasam ya zartar da hukuncin a wata kara da aka
shigar da Secondus kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kotun
ta kuma dakatar da shi daga gudanar da taron kananan hukumomi da na mazabu har
sai an kammala sauraren karar.
Ibeawuchi
Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da Umezirike Onucha, wadanda
kusoshi ne a jam’iyyar ta PDP suka shigar da PDP da Secondus kara a cewar
jaridar Vanguard.
A
dai watan Dismbar shekarar 2017 aka zabi Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar
a babban taron da jam’iyyar ta yi a Abuja.
Hakan
na nufin sai a watan Disambar bana wa’adinsa zai kare, amma masu adawa da
mulkinsa, wadanda ke zarginsa da wargaza tafiyar jam’iyyar, sun nemi ya sauka
daga mukamin, suna masu cewa shi ne musabbabin da ya sa ake ta fita daga
jam’iyyar, zargin da Secondus din ya musanta.
Rahotanni
baya-bayan sun ce an ba Secondus zabin ya shirya babban zaben jam’iyyar a watan
Oktoba mai zuwa, amma ya yaki, yana mai cewa sai ya kammala wa’adinsa kafin ya
sauka.
A
‘yan makwannin da suka gabata ne wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta
PDP da aka fadada a Abuja, ya yanke shawarar katse wa’adin mulkin Secondus a
watan Oktoba domin neman mafita ga rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa
a jam’iyyar.
0 Comments