Ku Daina Bari Ana Kashe Ku, Ku Rike Bindiga Ku Kare Kanku -Sakon Masari Ga Al'umma


Daga Zaharaddeen Abbas

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari  cikin fushi ya bukaci jama’ar jihar dake fuskantar hare haren ‘yan bindiga da su nemi makamai domin su kare kan su daga cin kashin da 'yan bindiga ke yi musu. 

Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Jibia domin jajantawa al’ummar garin sakamakon kashe mutane goma da jami’an Kwastam suka yi a kan shinkafa, duk da hukumar Kwastan din sun ce bisa hatsari hakan ya faru. 


Gwamnan ya ce ba daidai bane mutane su mika wuyar su ga ‘yan bindiga suna kashe su ba tare da sun yi wani kokarin kare kan su ba ana musu kisan gilla a koyaushe. 

Sanarwar da Daraktan yada labaran Gwamnan Abdu Labaran Malumfashi ya gabatar ta ce rashin jajircewar jama’a wajen tunkarar ‘yan bindigar na kara ba su damar afka musu akai akai, inda yake cewa lokaci ya yi da jama’a za su cire tsoro su fahimci cewar sha’anin tsaro ba aikin gwamnati bane ita kadai.


Masari har wala yau ya ce gwamnatin Katsina na bin matakan da suka dace domin ganin an bi kadin kisan gillar da jami’an Kwastam suka yi wa jama’ar jihar da kuma wadanda suka jikkata sakamakon lamarin.

Gwamnan ya gargadi ‘yan'uwa da iyalan wadanda aka kashe cewar kar su yarda da wata yaudara daga hukumar Kwastam domin kuwa yanzu haka lauyoyin gwamnati na nazari akan matakan da ya dace su dauka domin tabbatar da ganin an musu adalci.

Masari ya kuma ce abin da jami’an Kwastam ke yi ya saba ka’ida saboda haka ba za su lamince da haka ba.

Post a Comment

0 Comments