Ku Yafe Mana -Cewar Tubabban 'Yan Boko Haram Ga 'Yan NijeriyaWasu daga cikin kwamandodin Boko Haram da suka ajiye makaman su suka kuma mika kan su ga sojojin Nijeriya sun roki jama’ar kasar da su gafarta musu akan ayyukan da suka yi.

Daraktan yada labaran rundunar sojin kasa, Janar Onyema Nwachukwu yace cikin wadanda suka nemi gafarar harda babban masanin hada bama baman kungiyar Musa Adamu da ake yiwa lakabi da Mala Musa Abuja da mataimakin sa Usman Adamu da ake yiwa lakabi da Abu Darda.

Yayin gabatar da tubabbun ga manema labarai, tsoffin mayakan sun dauki rubuce rubucen dake cewa, ‘Yan Najeriya, ku yafe mana’.


Mukaddashin kwamandan runduna ta 7 ta sojin Najeriya Birgediya Janar Abdulwahab Adelokun Eyitayo na daga cikin wadanda suka halarci bikin mika tubabbun a Runduna ta musamman ta 21 ta sojin Najeriya dake Bama.


Janar Eyitayo ya yabawa tubabbun da suka aje makaman su, yayin da ya bukace su da suyi magana da ‘yan uwan su domin ganin suma sun rungumi zaman lafiya wajen dawowa cikin jama’a domin sake rayuwar su.

Kwamandan ya ce za a sake horar da tsoffin mayakan kamar yadda gwamnatin Najeriya ta tsara, yayin da aka raba musu kayan sawa da kayan abinci.

Akalla mayakan boko haram 335 da iyalan su 746 suka aje makaman su a Jihar Borno.

Post a Comment

0 Comments