Ku Yi Hakuri, Kar Ku Dauki Fansa- Gwamna Lalong


Gwamnan Jihar Filato Simon Bako Lalong ya sha alwashin hukunta duk wadanda ke da hannu a rikice rikicen da ake samu a Jihar sa da zimmar hana zaman lafiya.

Yayin da yake tsokaci bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kashe matafiyan da aka yi da kuma tashe tashen hankulan da suka biyo baya, Gwamnan ya ce yanzu haka hankalin jama’a ya fara kwanciya, kuma nan bada dadewa ba za a rage dokar hana fitar da aka sanya a wasu yankuna.

Lalong ya ce matakan da suke dauka sun hada da gudanar da bincike na hakika domin tabbatar da masu aikata laifuffuka, kuma jami’an soji da ‘yan Sandan dake samun umurni daga fadar shugaban kasa na gudanar da ayyukan su bisa ka’idar doka.

Gwamnan ya ce tun da ya kafa dokar hana fita ta sa’oi 24 ana ci gaba da samun ci gabar kwanciyar hankali, kuma ko a wannan makon yana saran sake rage dokar domin baiwa jama’a damar gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Lalong ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya masa alkawarin taimakawa wadanda rikicin ya rutsa da su a jihar da kuma wadanda suka rasa matsugunin su.

Gwamnan ya ce ya kuma roki shugaban kasar akan tallafawa wadanda suke zama a sansanin ‘yan gudun hijira sakamakon rasa gidajen su saboda yawan da suke da shi, kuma shugaban ya ce zai yi magana da ma’aikatar jinkai ta kasa akai.

Gwamnan ya ce kokarin da suke na zaman lafiya ya taimaka wajen zaman lumana na shekaru 6 kuma ba zasu bari wani ya kawo musu tsaiko ko haifar da tashin hankali ba.

Post a Comment

0 Comments