BBC Hausa ta labarto cewa; Kungiyar Kiristoci Ta Najeriya CAN reshen jihar Filato a yankin tsakiyar kasar, ta yi Allah-wadai da kashe mata...
BBC Hausa ta labarto cewa; Kungiyar Kiristoci Ta Najeriya CAN reshen jihar Filato a yankin tsakiyar kasar, ta yi Allah-wadai da kashe matafiya da aka yi a kan titin Rukuba a ranar Asabar.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar a jihar Polycarp Lubo ya fitar a ranar Lahadi, ya nemi jami’an tsaro da su gano wadanda suka aikata hakan.
A ranar Asabar ne wasu bata gari suka tare motocin bas na wasu matafiya da rahotanni suka ce Musulmai ne, inda suka kasha mutuum 22 tare da ji wa wasu da dama rauni.
Mr Lubo ya kuma yi Allah-wadai da kasha-kashen da ake yi Bassa da Riyom a karamar hukuar Jos Ta Kudu da kuma karamar hukumar Barkin Ladi.
Ya ce: “Muna nuna alhininmu da takaicinmu kan hare-haren baya-bayan nan na Riyom da Jos Ta Arewa da Barakin Ladi da kuma Bassa, da suka jawo asarar rayuka.
“Shugabancin CAN ya yi tur da wadannan hare-haren yana kuma rokon jami’an tsaro da su tabbatar da dawowar doka da oda.
“Kowace rai na da muhimmanci kuma ba za a yarda da kashe mutane don bambancin addini ko kabilarsu ba,” in ji shi.
No comments