Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwamitin Zagayen Maulidi Ya Kai Tallafin Magani Asibitn Funtua

Daga Hussaini Yero, Funtuwa. Kwamitin zagayen Maulidin Annabi (SAW) karkashin Zawiyyar Sheikh Abubukar Alti Funtuwa, sun kai tal...


Daga Hussaini Yero, Funtuwa.

Kwamitin zagayen Maulidin Annabi (SAW) karkashin Zawiyyar Sheikh Abubukar Alti Funtuwa, sun kai tallafin magani a Asibitin Tudun Wada Funtuwa domin tallafawa masu fama da annobar gudawa da amai.

Shugaban kwamitin lafiya na zagayen Maulidin, Malam Hafizu Tukur da  Sakataren Babban Kwamitin Zartarwar, Ibrahim Bawa da sauran membobin ne suka jagoranci mika tallafin maganin ga Shugaban Asibitin. 

A jawabinsa Malam Hafizu Tukur ya bayyana cewa, kwamitin zagayen maulidin na 'Yan Funtua da Zawiyyar Sheikh Abubukar Alti ke gudanarwa a duk shekara, karkashin jagorancin Khalifa Ali Saidu Alti; "muka kawo ma 'yan'uwanmu da annobar gudawa da Amai ya same su albarkacin Sayyidina Rasulillahi (SAW). Da fatan Allah ya ba su lafiya, ya kuma kawo mana karshen wannan Annoba". 

A nasa jawabin, Sakataren Kwamitin a madadin Shugaban Babban Kwamitin, Bishir Muhammad Funtuwa ya bayyana cewa, wannan Kwamitin zagayaen Maulidin yana gudanar da ayyukan jinkai da tallafawa marasa karfi da ziyarar gidan Yari da da dai sauran su.

Shugaba Mai kula da Asibitin Tudun Wada Funtuwa, Lawal Shehu Auta, ya bayyana godiyarsa ga Kwamitin zagayen Maulidin Annabi da ya kawo musu gudunmuwar magunguna; " kuma wannan tallafin ya zo a lokacin da ya dace, kuma zai taimaka wajen ceton rayuwar mutane da dama", inji shi.

Kuma ya yi kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan Kwamitin zagayalen Maulidin Annabi domin tallafawa marasa lafiyar gudawa da amai.

No comments